Gwamnan APC ya fara bugun-kirji, ya hango nasara tun da babu wanda ya saye fam


Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya maida fam din da ya saya na sake neman takarar kujerar gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar APC. Legit.ng ta ruwaito.

Premium Times ta ce a ranar Talata, 10 ga watan Mayu 2022, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya maida fam din da ya cike a babban dakin taro na ICC a Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai a jiya, Babajide Sanwo-Olu ya nuna cewa ya na mai sa ran za a sake zaben shi saboda ayyukansa da aka gani a shekaru uku.

Gwamnan ya fadawa ‘yan jarida cewa gwamnatinsa ta yi nasarar canza halin da Legas ke ciki, duk da annobar COVID-19 da aka yi fama da ita na dogon lokaci.

“Mun bunkasa garin nan a kan yadda aka san shi a shekaru uku zuwa hudu kafin mu karbi mulki. Yanzu ya fi kowane samun kudi daga waje saboda an samu tsaro.”

Babu mai neman tikiti a APC?

Legit.ng Hausa ta fahimci babu wani wanda ya yanki fam din neman Gwamna a Legas bayan Sanwo-Olu. Hakan na nufin kai-tsaye gwamnan zai samu tuta.

A tarihin jihar Legas kuwa, PDP ba ta taba karbe mulki ba tun da aka dawo tsarin farar hula a 1999. Sanwo-Olu ne gwamna na hudu da aka yi a shekara 20.

Idan za a tuna, shekaru hudu da suka wuce Akinwumi Ambode ya rasa samun tikitin jam’iyyar APC duk da yana kan kujerar gwamna, hakan ta sa bai zarce ba.

Kamar yadda TVC ta kawo rahoto, wani gwamna mai neman tazarce da babu wanda ya yi tarayya da shi wajen sayen fam shi ne Babagana Umara Zulum.

Taron ‘Yan siyasan Yarbawa a kan 2023

Vanguard ta ce Sanwo-Olu ya yi magana a kan zaman da aka yi da masu neman shugaban kasa a jam’iyyar APC daga yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Sanwo-Olu ya ke cewa Bisi Akande da Segun Osoba su ka kira wannan taro da kusan kowa ya samu halarta, amma ba a iya samun abin da ake so a zaman ba.

Osinbajo ya karbu a Gombe

An ji cewa Yemi Osinbajo ya kai ziyara domin gaida Mai martaba Sarkin Gombe, Abubakar Shehu Abubakar a fadarsa bayan ya hadu da 'ya 'yan jam'iyyar APC.

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya nuna goyon bayansa ga takarar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yake son yi a zaben 2023.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN