APC ta rufe sayar da Fam, Zulum da gwamnoni biyu ba su da abokan hamayya


Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta rufe sayar da Fam din takara ga masu neman kujerar mulki karkashin lemarta a zaben kasa da za'a yi a 2023.

Jam'iyyar ta fara sayar da Fam din ne ranar 26 ga watan Afrilu, 2022.

APC ta sayar da na shugaban kasa milyan 100. A cikin kudin N30m na takarar ayyana niyya ne, N70m kuma kudin takardar neman kujeran ne.

Na gwamna kuwa, ta sayar da Fam din N50m yayinda masu neman kujerar Sanata N20m.

N10m ta sayar da Fam ga masu neman kujerar majalisar wakilai sannan masu neman takarar kujerar majalisar jiha N2m.

Kawo ranar rufe sayar da Fam din, gwamnoni uku basu da abokan hamayya a zaben.

Sune Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum; Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahaman Abdulrazak.

A sabon jadawalin da jam'iyyar ta saki da daren Litnin, ta umurci dukkan wadanda suka karbi Fam su cike kuma su dawo da shi ranar Laraba, 11 ga Mayu, 2022.

Bayan haka ranar Juma'a za'a fara tantance Gwamnoni, yan majalisar wakilai, Sanatoci da shugaban kasa ranar Asabar, 14 ga Mayu, 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN