Wata Amarya ta bace a ranar daurin aurenta a jihar Neja, don haka aka ci gaba da daurin auren inda kanwar amaryar ta maye gurbin Amarya.
‘Yan uwan ma’auratan sun hallara a ranar Juma’a, 13 ga watan Mayu, domin daurin auren a garin New Bussa da ke jihar Neja, inda suka lura cewa Amaryar ta bata.
Da aka tambayi abokan Amaryar, sun bayyana cewa Amaryar ta yi nuni da cewa za ta je wani wuri ta buya na dan wani lokaci saboda ba ta da sha’awar yin aure.
Iyalan Amarya sun yi ganawar sirri nan take inda daga bisani suka gayyaci dangin ango zuwa taron, kamar yadda jaridar Borgu Online ta ruwaito.
Iyalan biyu sun amince cewa za a ci gaba da daurin auren tare da kanwar amaryar a matsayin sabuwar Amarya.
Rahotanni sun ce kanwar ta amince ta auri Angon ‘yar uwarta kuma aka daura auren.
An ce Amaryar da ta maye gurbinta tana murna da "mijin da Allah ya ba ta."
Rubuta ra ayin ka