2023: Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara ya janye daga takarar gwamna a PDP


Gabanin zaben fidda gwani na gwamna na jam'iyyar PDP, tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau ya fice daga takarar.

Channels Tv ta rahoto cewa, Mahdi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatarensa Umar Aminu a Gusau babban birnin jihar Zamfara ranar Laraba.

Mahdi Gusau ya bukaci deliget-deliget, shugabannin jam’iyyar, da magoya bayansa da su zabi Dr. Lawal Dauda ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar ta Zamfara.

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana dalilinsa na ficewa daga takarar ba.

Ba Mahdi kadai aka samu daga PDP cikin wadanda suka janye daga takarar gwamna ba, Channels Tv ta ruwaito cewa, dan takarar gwamnan jihar Abia na PDP, Sanata Abaribe shi ma ya janye daga takara.

Idan baku manta ba, rahotannin Legit.ng Hausa a baya sun kawo yadda aka tsige Barista Mahdi Aliyu Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara a watan Fabrairun wannan shekara bayan sauya shekar mai gidansa daga PDP zuwa APC.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN