Iyalan fasinjojin da aka sace yayin da suke kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun balle zanga-zanga a babban birnin tarayya ta Abuja.
Wannan ne karo na farko da 'yan uwan wadanda aka sacen suka fito zanga-zanga tun bayan faruwar ibtila'in, Punch ta ruwaito.
A ranar 28 ga watan Maris din 2022, 'yan ta'adda sun kai mugun hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna kuma hakan ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum takwas yayin da 26 suka jigata kuma aka yi garkuwa da wasu.
Iyalan sun ce zanga-zangar sun fito ta ne sakamakon barazanar da 'yan ta'adda suka yi na cewa za su fara halaka wadanda ke hannunsu idan har ba a cika sharuddansu.
Sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, hafsoshin tsaro da kungiyoyin duniya da su kawo musu dauki.
Karin bayani na nan tafe...
AK9Train: Miyagu sun tuntubi kakakin Sheikh Gumi, sun ba FG wa'adin kwana 7 ko su aiwatar da nufinsu
Rubuta ra ayin ka