Bashar Ishaka - Birnin kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta Umurci Shuwagabannin ƙananan hukumomi da na Yankunan cigaba da su tantance sahihan manoma domin tallafa musu don ƙara inganta ayukkan noma a jihar Kebbi.
A wani zama da ya gudana a ɗakin taro dake Ma'aikatar Ƙananan hukumomi da masarautu dake Birnin Kebbi, inda zaman ya samu halartar Kwamishinoni uku da Sakatarorin dindindin dinsu da suka hada da Hon. Hassan Shallah (Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu) Hon. Mai Gari Abdullahi Ɗakin Gari (Kwamishina noma) da kuma Hon. Aminu Garba ( Kwamishinan Ma'aikatar Kula da dabbobi).
An kuma yi kira ga shuwagabannin da wannan nauyin ya rataya a wuyansu da su tabbatar da cewa mutanen da zasu bayar manoma ne na gaske da basu taɓa cin gajiyar tallafin gwamnati ba kowane iri ne.