Wasu ‘yan bindiga sun kai hari Masallaci a Taraba a lokacin buda baki suka kashe mutane uku


Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a wani Masallaci sun kashe mutane uku a lokacin da masu ibada ke buda baki a ranar Talata 5 ga watan Afrilu. 

Aminiya ta ruwaito cewa ‘yan bindigar da adadinsu ya kai 50, sun kashe mutane uku a cikin masallacin, sannan kuma sun yi awon gaba da mutanen kauyen da dama wadanda aka kai su inda ba a sani ba.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a kauyen Baba Juli da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba.

Wani dan kauye yace; 

“Harin na jiya ya kama mu ba tare da sani ba. Muna buda baki ne a cikin masallacin sai muka fara jin karar harbe-harbe, kuma babu wani abin da za mu iya yi don dakile ‘yan ta’adda”.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce yana jiran karin bayani daga ofishin ‘yan sanda na Bali.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN