Yanzu yanzu: Abubakar Malami ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Gwamnan jihar Kebbi a 2023


Magoya bayan babban Lauyan Gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a Abubakar Malami, sun tara kudi naira miliyan 130 a matsayin goyon bayansu ga kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Kebbi a 2023, jim kadan bayan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a karkashin jam’iyyar APC. 

Bayanai na cewa mata magoya bayan Malami a jihar sun ba da gudummawar Naira miliyan 30 yayin da kungiyar Malami Women Support Initiative (MAWOSI) ta bayar da Naira miliyan 20. Shugabar kungiyar ta MAWOSI, Hon.Halima Hassan Tukur ce ta sanar da bayar da gudummawar guda biyu.

Kungiyar kansiloli da ke karagar kujerarsu a halin yanzu su 225 na jihar Kebbi, ta bayar da gudunmawar Naira miliyan 25, ita kuma kungiyar tsaffin ‘yan majalisar dokokin jihar ta bayar da naira miliyan biyar. 

Har ila yau, wadanda suka ci gajiyar lamunin AGSMIES da Honarabul Atoni Janar na Tarayya ya bayar sun ba da gudummawar tsabar kudi Naira miliyan biyar a matsayin gudummawa ga kudirin Ministan. 

Yayin da abokansa da mukarrabansa suka bayar da gudunmawar Naira miliyan 50. An bayyana tallafin a wani taron da aka yi a Birnin-Kebbi babban birnin jihar inda Ministan ya bayyana aniyarsa a gaban masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sa. 

A jawabinsa a wajen taron, Malami ya bayyana cewa ya kasance jakadan da ya cancanta a jihar Kebbi yayin da yake yiwa kasa hidima a matakin Majalisar zartarwa ta tarayya a matsayin Ministan shari’a kuma babban Lauyan Gwamnatin tarayya.

Ya bayyana cewa yana fuskantar matsin lamba daga jiga-jigan magoya bayansa da kuma al’ummar jihar Kebbi masu kishin kasa suna kiransa da ya tsaya takarar Gwamna a jihar.

Ya yi nuni da cewa yana da ma’ana domin ya ga ya zama wajibi a tuntubi masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar domin su ba shi shawarwarin da za su taimaka wajen samar da ci gaban jihar nan gaba. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN