Wasu ‘yan ta’adda sun kashe uku daga cikin mutane 26 da suka yi garkuwa da su a Angwan Bulus da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna saboda gazawar iyalansu wajen biyan kudin fansa N20m.
'Yan ta'addan sun kuma yi barazanar kashe wasu da suka sace musamman mata idan ba a biya musu bukatunsu ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Talata.
“Na samu waya da wasu mutane a safiyar yau gawarwaki uku da aka gano a kauyen Dutse a wani wuri a cikin daji, an kwashe gawarwakin zuwa asibitin Saint Gerald, muna kokarin tattaunawa da kwamandan yansandan yankin domin tabbatar da an dawo da wadanda suka rage a hannun miyagun,” in ji PPRO.
An tattaro cewa da misalin karfe 8 na daren ranar 31 ga watan Maris, ‘yan bindigar sun kai hari a unguwar Angwan Bulus, inda suka kashe mutane biyu tare da sace wasu mutane 26. Daga cikin wadanda abin ya shafa har da wata mata da ‘ya’yanta hudu.
Wata majiya mai tushe a yankin da ta tabbatar da faruwar lamarin ta shaida wa Daily Sun cewa barayin sun Kira yanuwan wadanda suka sace suka ce su je wani wuri a kauyen Dutse da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja domin dauko mutanen uku da suka kashe saboda rashin biyan kudin fansa.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “’yan bindigar sun kira da safiyar jiya cewa sun kashe uku daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su, inda suka shaida mana inda aka ajiye gawarwakinsu.
“Yan ta’addan sun kira da yammacin jiya, suka ce tunda mun ki biyan kudin fansa, mu je wani wuri mu dauki gawarwakin mutanenmu.
“Kafin mu isa wurin, mun samu labarin cewa tuni ‘yan sanda suka kwashe gawarwakin sun ajiye su a Asibitin Katolika na Saint Gerald, da ke unguwar Kakuri, Kaduna, mun kasance a asibitin jiya da daddare domin tabbatar da hakan.
'Yan ta'addan sun kara yin barazanar cewa idan al'umma da iyalai suka kasa biyan kudin fansa zuwa gobe da yamma ( Talata da yamma), to su je wuri da aka ajiye gawakin farko domin su dauki gawarwakin yanuwansu. .
Shugaban Ungwan Bulus, Gideon Haruna Goni, shi ma ya tabbatar wa manema labarai hakan.
"Sun yi barazanar kashe wasu musamman mata idan ba a biya musu bukatunsu ba, an sace 26, an sako daya, an kashe uku, wanda aka sako ya dogara ne akan rashin lafiya, yana da matsalar hanta." Goni yace.
“Ina kira gare su da kada su kashe kowa, muna kira ga Gwamnatin jiha da tarayya da Malaman addini da su kawo mana dauki domin a daina kashe-kashen.
Daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da ‘yan uwansu, ya ce sun samu damar tara N7m, amma ‘yan ta’addan sun dage a kan Naira miliyan 20 ko kuma za su ci gaba da kashe wadanda aka kashe.