Da duminsa: Shugaba Buhari ya amince da sake bude wasu iyakokin kasa guda hudu har da na Kamba a jihar Kebbi


Rahotanni daga Abuja na tarayyar Najeriya na cewa  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake bude wasu iyakokin kasa guda hudu. Iyakokin su ne Idiroko a Ogun, Jibiya a Katsina, Kamba a Kebbi da Ikom a Cross River. Shafin isyaku.com ya samo.

Idan za a iya tunawa, a wani mataki na dakile yawaitar shigo da magunguna da kananan makamai da kayayyakin amfanin gona zuwa Najeriya ba bisa ka'ida ba daga kasashen yammacin Afirka, a watan Agustan 2019, shugaba Buhari ya bayar da umarnin rufe iyakokin kasa.

A shekarar 2020, shugaban kasar ya bayar da umarnin sake bude iyakokin a Seme a Legas, Illela a Sakkwato, Maigatari a Jigawa, da Mfum a Cross River.

Wata takarda da mataimakin kwanturola-janar na NCS, E, I. Edorhe, ya fitar a ranar 22 ga Afrilu, ya bayyana cewa shugaban kasar ya bayar da umarnin sake bude iyakokin.

“Sakamakon umarnin shugaban kasa na ranar 16 ga Disamba, 2020, na ba da izinin sake bude kan iyakokin kasa na Mfum, Seme, Illela da Maigatari a fadin kasar nan, an umurce ni da in sanar da ku cewa an amince da sake bude wasu karin kan iyakokin hudu da aka jera a kasa don sake bude: Idiroko kan iyaka, jihar Ogun (yankin kudu maso yamma); Jibiya bakin iyaka, Katsina ( shiyyar arewa maso yamma); Kamba kan iyaka, jihar Kebbi ( shiyyar arewa maso yamma); da kuma iyakar Ikom, jihar Cross River (shiyya ta kudu da kudu),” in ji sanarwar.

Don haka, duk tsarin kwastam da JBPTs su lura da kuma tabbatar da cewa an gudanar da aikin da ya dace daidai da ƙa'idodin aiki.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN