SANARWA: Zargin kama yara yan shekara 6 da Sifeto ya yi a jihar Kebbi, sashen SCID sun fara bincike bisa umarnin Kwamishinan yan sandan


Hukumar yansandan jihar Kebbi karkashin umarnin Kwamishinan yan sandan jihar ta fara binciken kwakwaf kan zargin kama wasu kananan yara da wani Safeto ya yi a garin Kamba.

Fitowar wani faifen bidiyo da ya samo asali daga shafin labarai na isyaku.com ya nuna yadda wani Lauya da ke tsaya wa yaran ya yi jawabi yadda yake zargin lamarin ya faru, bayan fitowarsu a Kotun Sharia ta 1 a garin Birnin kebbi.

Tuni dai wannan bidiyo ya zama abin kallo kuma zance da jama'ar Arewacin Najeriya ke tattaunawa, musamman a shafukan sada zumunta.

Sakamakon haka hukumar yansandan jihar Kebbi, ta hannun Kakaknta SP Nafi'u Abubakar, ta mayar da martani kan zargin a wata takarda da ta fitar tare da sa hannun Kakakinta amadadin Kwamishinan yan sandan jihar Kebbi.

Karanta cikakken sanarwar yan sanda dangane da lamarin:

"An jawo hankalin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi kan wani faifan bidiyo da ke yawo a wasu kafafen sada zumunta inda wani Bar. Bashir ya yi jawabi ga manema labarai inda ya zargi Sifeto Ilyasu Alhassan da damke wasu daliban makarantar Alif International Academy da ke Kamba bisa laifin kutsawa cikin gidansa tare da satar wayarsa ta wutan lantarki da darajarsa ya kai Naira dubu dari biyu da hamsin (N250,000) kacal. Ya ci gaba da zargin cewa, Sifeton ‘yan sandan ya bukaci daliban da abin ya shafa da su amsa laifinsu tare da alkawarin ba su kudi Naira Dubu Biyu (N2,000) kacal.

Dangane da abin da ya faru, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi, CP. Musa Baba, psc(+) ya umurci mataimakin kwamishinan ’yan sanda na SCID, Birnin Kebbi, da ya gudanar da bincike na gaskiya game da wannan zargi da nufin bankado al’amuran da ke tattare da wannan zargi.

Don haka rundunar ta yi amfani da wannan kafar domin tabbatar wa al’ummar jihar Kebbi nagari da son zaman lafiya cewa, sakamakon binciken da aka gudanar zai bayyana ga jama’a. A halin yanzu, yana da mahimmanci a sake nanata cewa, umarnin ba zai bar wata kafa ba wajen daukar matakin da ya dace kan duk wani ma'aikacin da ya yi kuskure.

SP. NAFI'U ABUBAKAR, anipr

JAMI'IN HULDA DA  JAMA'A,

AMADADIN:- KWAMISHINAN YAN SANDA JIHAR KEBBI".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN