Mafarauci ya bindige Limamin garinsu har Lahira, ya ce ya dauka cewa Barewa ne


Rundunar yan sanda a Jihar Osun ta kama wani mafarauci wanda ake zargi da bindige tare da kashe wani limamin kauyen Alagunan a karamar hukumar Aiyedaade, wanda ya yi zaton naman daji ne, The Punch ta rahoto.

Jaridar Vanguard ita ma ta rahoto cewa mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Yemisi Opalola, ce ta sanar da hakan yayin holen wanda ake zargin a hedkwatar rundunar a Osogbo, ranar Talata.

Ta ce:

"A ranar 17 ga watan Afrilu, misalin karfe 11.30 na safe, wani mai korafi daga Ogbere Oloba a Ibadan ya zo caji ofis inda ya ce wani mafarauci daga kauyensu ya bindige mahaifinsa, Adegun Yusuf, 78, limamin kauyen Alaguntan a Orile-Owu kuma ya mutu.

"Daga bisani an kama wanda ake zargin kuma ya amsa laifin da ake zarginsa.

"Ya yi bayanin cewa ya tafi farauta ne sai ya hangi Barewa a cikin daji kuma ya harbe ta da bindigarsa ta mafarauta.

"Ya yi mamakin da ya tafi ya dauki barewan, kawai sai ya tarar da Baba Liman a kasa. Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike."

A wani labarin, Alhaji Lukman Shittu, wani malamin addinin musulunci a Oyo ya yi zargin cewa wani daga cikin wadanda suke sallah a masallacinsa ya ɗirka wa matarsa ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan zargin ne yayin da ya ke bayani ga kotun kwastamare Grade A da ke zamanta a Mapo, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Shittu, wanda matarsa ta yi kararsa na neman saki, ya shaida wa kotun cewa matarsa tana bin mazaje kuma ta haifi ƴaƴa uku da bai da tabbas nasa ne, rahoton Daily Trust.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN