Da duminsa: Matasa sun fatattaki wani dan Majalisa sun kore shi kuma suka bi shi da gudu a mazabarsa (Bidiyo)


Rahotanni sun ce an kori wani dan majalisar dokokin jihar Ondo da gudu daga garin Owo bisa zargin rashin gudanar da aikin ga jama'a . Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Wani ma’abocin Facebook, Tosin Fapohunda II wanda ya raba bidiyon, ya yi ikirarin cewa dan majalisar shi ne shugaban masu rinjaye na jihar Ondo, Honourable Ogunmolasuyi AKA West.

Ya rubuta; 

A yau ne matasan mazabarsa suka fatattaki wani dan majalisar jihar Ondo kamar barawo sakamakon rashin gudanar da aiki da kuma kadaitaka daga mazabarsa tun bayan da aka kada masa kuri'a da ya kai shi zauren majalisar dokokin jihar Ondo.

Wasu matasa a mazabarsa sun fatattaki shugaban masu rinjayen na jihar Ondo Honorabul Ogunmolasuyi AKA West daga mahaifarsa sakamakon zargin yin watsi da jamaarsa tun lokacin da aka zabe shi da rashin aikin yi."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN