Kotu a Kano ta tsare wata tsohuwa mai shekaru 107 da matashi saboda kwakwale idon wani Almajiri


Wata Kotun Majistare da ke Kano, ta bayar da umarnin tsare wata mata mai suna Furera Abubakar mai shekaru 107 da kuma Isah Hassan mai shekaru 17 a gidan gyaran hali bisa zarginsu da cire kwayar idon wani yaro dan shekara 12. 

Shafin isyaku.com ya ruwaito cewa, a ranar 29 ga watan Maris ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wadanda ake tuhuma da cire kwallon idon dama na wani yaro Almajiri domin dalilan aikata layan baduhu. 

Ana zargin Isah, wanda ake kara na farko, da ya kawo idon mutum da za a yi amfani da shi wajen shirya wata laya ta “Baduhu ko layar zana” .

Lauyan masu shigar da kara, Lamido Soron-Dinki, ya shaida wa kotun a ranar Laraba 6 ga watan Afrilu cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Maris a Rimin Hamza Quarters, da ke karamar hukumar Tarauni a jihar Kano.

Abubakar da Isah mazauna unguwar Dantsinke da ke Kano, suna fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume biyu da suka hada da hada baki da kuma yunkurin aikata kisa.

Soron-Dinki ya yi zargin cewa a wannan rana da misalin karfe 9:00 na dare, wadanda ake tuhumar sun hada baki, suka yaudari Mustapha Yunus zuwa wani rafi da ke kusa tare da kwakwale idonsa na dama da wuka mai kaifi.

“Sakamakon haka, yaron ya samu munanan raunuka inda aka garzaya da shi Asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda aka kwantar da shi domin yi masa magani.

A cewar mai gabatar da kara, laifukan sun sabawa tanadin sashe na 97 da 229 na kundin laifuffuka.

Daga nan ne babban alkalin kotun, Muhammad Jibril, ya bayar da umarnin a garkame wadanda ake kara a wani gidan gyaran hali.

Jibril ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 11 ga watan Afrilu. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN