Hotunan mazauna kauyukan Zamfara suna gudun hijira saboda tsanantar harin yan bindiga


Mazauna kauyen Magazu da kewaye a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun fara barin gidajensu na gado sakamakon tsanantar farmakin 'yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.

Legit ta labarta cewa wasu daga cikin mazauna yankunan an gansu tsaitaye a bakin titi da 'ya'yansu, kayansu a daddurae da dabbobinsu biye da su, TVC News ta ruwaito.

Sun sha alwashin ba za su sake komawa gidajensu ba har sai tsaro ya tabbata a yankin.

Yankin Magazu ya kasance madaddalar 'yan bindiga inda suka matsantawa domin kua tun ranar Litinin da ta gabata suka kai farmaki har zuwa yau babu sauki, lamarin da ke cigaba da kawo rashin rayuka da salwantar dukiyoyi.

Hukumomin 'yan sanda na jihar Zamfara a ranar Talata da ta gabata sun tabbatar da sace mutum ashirin da hudu da suka hada da mata da kananan yara, kuma har yanzu suna hannun miyagun.

Wannan lamarin na zuwa ne kasa da sa'o'i 12 bayan 'yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyukan.

Mazauna kauyen sun koka kan yadda ba a samun jami'an tsaro suna kai musu dauki duk kuwa da yadda 'yan bindigan ke dadewa suna cin karensu babu babbaka.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN