2023: An karba wa Tinubu fom din takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC


Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya karbi fom din N100m na jam’iyyar APC domin tsayawa takarar shugaban kasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Vanguard ta ruwaito cewa, jiga-jigan kungiyar goyon bayan Tiubu ta TSG ce ta dura cibiyar taron kasa da kasa ICC domin sayen fom din a madadin Tinubu.

An tattaro cewa Tinubu, wanda ya tafi kasar Saudiyya aikin Hajji, ya samu wakilcin wasu makusantan sa da suka hada da dan majalisar wakilai daga mazabar tarayya ta Ikeja, James Faleke

Hakazalika da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Agege a zauren majalisa, Babatunde Adejare; da kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.

Faleke da Lawal da sauran masu biyayya ga jigo a siyasar jihar Legas ne suka karba masa fom din takarar shugaban kasa a hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa da ke titin Blantyre, Wuse 2, Abuja, da misalin karfe 3 na rana.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN