Hon Abubakar Bello da aka fi sani da Abu Najakku ya yanta Fursunoni uku a jihar Kebbi


Hon Abubakar Bello wanda aka fi sani da Hon Abu Najakku, ya yanta Fursunoni uku daga Kurkukun garin Birnin kebbi a cikin watan Ramadan bayan ya biya Tara na kudi da Kotu ta yi masu.

Wadanda aka yanta sun hada da Abdulrasheed Bala Ambursa, Manir Abubakar Birnin kebbi, da Ahmad Nura Gwadangaji suna zaman wakafi a Kurkuku ne bayan sun kasa biyan kudin Tara da Kotu ta yi masu kan laifuka da suka aikata.

Hon. Bello Dan Tsoho da Bello Utono ne suka wakilci Hon Abubakar Bello (Hon Abu Najakku) wajen aiwatar da samun nassarar yanta Fursunonin.

Hon Bello Dan Tsoho tare da Bello Utono sun yi wa wadanda aka yanta nasiha na ganin sun ci gaba da zama na gari a cikin al'umma tare da kauce wa duk wani lamari na rashin gaskiya za zai iya sake jafa su cikin wata lalura irin wannan.

Ko a bara dai, Hon Abubakar Bello Na Jakku ya yanta wasu Fursunoni daga Kurkuku a garin Birnin kebbi a irin wannan watan na Ramadan .

Hon Abu Najakku ya tsaya takarar neman kujerar Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza a Majalisar Wakilai na tarayya a 2019. 

Babban ma'aikacin Gwamnatin tarayya ne a Abuja, kuma dan asalin garin Birnin kebbi da ke da tushe a Unguwar Kofar kola.

Mun samo cewa Hon Abu Najakku, mutum ne mai akidar gaskiya, mutunci da amana. Mai yawan kyauta da taimakon jama'a a ko'ina ya sami kansa.

Hon Abubakar Bello Abu Najakku

Wadanda aka yantar


Hon Bello Dan tsoho

Bello Utono

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN