“Ba za a yi zabe ba, kuma duk wanda ya yi yunkurin yin zabe zai mutu - Yan tsagerun kudu maso gabas


Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba da ke addabar manyan sassan yankin kudu maso gabashin Najeriya sun yi kira da a gaggauta sakin jagoran masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu. Sahara reporters ta ruwaito.

Kanu yana tsare a hannun hukumar DSS a hedkwatarta da ke Abuja, bayan da gwamnatin Najeriya ta dawo da shi gida daga Kenya a watan Yunin 2021, matakin da lauyoyinsa suka kira "ba bisa ka'ida ba."

Ana tuhumar sa ne a gaban kotu bisa tuhumarsa da laifin cin amanar kasa da ta’addanci a gaban kotu.

A cikin wani faifan bidiyo na mintuna 2 da dakika 55 da aka nada a wani daji, wani dan kungiyar ya ce ba za a yi zabe a yankin ba idan gwamnati ta gaza sakin Kanu.

“Mu ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba a kasar Biafra mun zo ne domin mu bayyana matsayar mu ga jama’a. Muna nan don kare ƙasarmu ta kowane hali. Ba mu da wani mai tallafawa. Kuma ba mu shirya samun ba,” inji shi.

“Ba mu a karkashin Simon Ekpa, DOS ko Uwazuruike. Duk wata gwamnati da ta ba wa daya daga cikin wadannan mutane kudi yana bata lokacinsa ne. Sakin Mazi Nnamdi Kanu ne kawai zai kwantar mana da hankali. Umarnin zaman-a-gida ranar Litinin yana nan daram . Babu wani abu da zai iya hana hakan in ban da sakin Mazi Nnamdi Kanu.

“Ba za a yi zabe ba, kuma duk wanda ya yi yunkurin yin zabe zai mutu. Su kuma jama’ar INEC me zai same ku idan muka same ku, Allah ne kadai ya sani, babu sauran fosta, fosta na siyasa a kasar Biyafara, idan kun gwada mu kuma aka fito yakin neman zabe, wuta za ta kone ku".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN