Da duminsa: Duba jerin sunayen kwamishinoni da hadiman Ganduje da suka yi murabus


A ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci wadanda ya nada mukaman siyasa da ke da burin yin takara a babban zaben 2023 da su ajiye mukamansu.

Ganduje ya basu daga yanzu zuwa ranar Litinin, 18 ga watan Afrilu domin su gabatar masa takardun murabus din nasu.

Sai dai kuma, tun kafin wa’adin da ya diba masu ya cika, wasu daga cikin kwamishinoninsa sun yi murabus daga mukamansu.

A wannan rahoton, Legit Hausa ta zakulo maku jerin kwamishinoni da hadiman da suka ajiye aikinsu domin yin takarar kujerun daban-daban

1. Murtala Sule Garo – Kwamishinan karamar hukuma da harkokin sarauta zai yi takarar kujerar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar APC

2. Musa Iliyasu Kwankwaso – Kwamishinan raya karkara zai yi kararar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Kura/Madobi/Garunmallam

3. Ibrahim Ahmad Karaye – Kwamishinan al’adu da yawon bude ido zai yi takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Karaye/Rogo

4. Nura Dankadai - Kwamishinan kasafin kudi zai yi takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Doguwa/Tudunwada

5. Sadiq Wali – Kwamishinan albarkatun ruwa zai yi takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP

6. Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya - Babban Darakta Hukumar Hisba ta Jihar Kano zai yi takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure

7. Hon. Sanusi Said Kiru - Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano zai yi takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Kiru da Bebeji a Jamiyyar APC

8. Dr. Mukhtar Ishaq Yakasai - Kwamishinan Ma'aikatar Ayyuka na Musamman na Jihar Kano zai yi takarar Majalisar Tarayya a Karamar hukumar Birni da Kewaye

9. Hon. Mahmoud Muhammad Santsi - Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano zai yi takarar Takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Gabawa da Gezawa a Jamiyyar APC

10. Malam Ali Bullet - Mai Bawa Gwamna Shawara akan Harkokin Sufuri zai yi Takarar Majalisar Jiha mai wakiltar Karamar Hukumar Tudunwada a Jamiyyar APC

11. Hon. Abdullahi M Gwarzo Babangandu - MD Remasab zai yi Takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Gwarzo da Kabo a Jamiyyar APC

12. Dr. Nasiru Yusuf Gawuna - Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi murabus a matsayin kwamishinan noma

13. Farouq Sule Garo - Babban mai ba gwamna shawara kan kula da ayyuka zai yi takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Gwarzo da Kabo a Jamiyyar APC

Mun kawo a baya cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya umurci dukkanin wadanda ya baiwa mukaman siyasa da ke son yin takara a zaben 2023 da su ajiye aiki.

A cikin wata sanarwa daga babban sakataren labaransa, Abba Anwar, a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, Ganduje ya ce an baiwa masu mukaman tsakanin yanzu da Litinin, 18 ga watan Afrilu su yi murabus, Daily Nigerian ta rahoto.

Ya ce umurnin ya yi daidai da tanadin sashi 84(12) na sabuwar dokar zabe.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN