Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce ta kama wasu da ake zargin ‘yan luwadi ne da ake zargin suna shirin gudanar da bikin auren ‘yan luwadi.
A cewar wani Mohammed Tijjani, an kama wadanda ake zargin ne a unguwar Gwange da ke jihar a ranar Asabar, 16 ga watan Afrilu.
Ya kuma mika godiyarsa ga kansilan unguwar Mashamari dake karamar hukumar Jere Hon Ibrahim Burma shuwa da kuma DPO na Gwange da suka yi gaggawar kama wadanda ake zargin. Karanta rubutun nasa a kasa:
"Ludu da Madigo haramun ne a al'adar kanem BORNO da ma duniya baki daya, hukunci daga mahangar addini na musulmi da kiristoci yana haifar da kisa da sauransu
."