Da dumi-dumi: Tsohon Gwamnan Zamfara Yari da Marafa sun sauya sheka daga APC zuwa PDP


Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Garba marafa sun sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Rahotun legit.

Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Ritaya kanal Bala Mande, ne ya sanar da hakan jim kadan bayan gama wani taron masu ruwa da tsaki a Gusau, babbar birnin jihar a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu.

Mande ya bayyana cewa sun zauna sannan sun yanke shawara kan batun sauya shekar Yari da Marafa sannan sun cimma yarjejeniyar aiki don ci gaban jam’iyyar.

Mande ya ce:

“Duk mun yarda za mu yi aiki don ci gaban jam’iyyar sannan PDP a jihar ta yi maraba da su a cikinta. Za mu tabbatar da gaskiya da adalci ga dukka mambobinmu har bayan mun lashe zabe a 2023.

“Za a sanar da ranar gagarumin bikin dawowarsu jam’iyyamu daga bisani amma za mu aiwatar da dukkan yarjejeniyar da muka cimma a yayin taron masu ruwa da tsaki.”

Sakataren labaran bangaren Yari na APC, Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji, ya tabbatarwa Daily Trust da ci gaban amma bai yi karin bayani ba.

Magaji ya ce:

“Eh, da gaske ne za mu koma jam’iyyar adawa ta PDP, kuma iya abun da zan iya fadi kenan a yanzu.”

A wani labari makamancin wannan, munji cewa kakakin majalisar dokokin Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Sulaiman, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic (PDP) mai mulki a jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Sulaiman ya lashe zabe a matsayin dan majalisa mai wakiltan mazabar Ningi a 2019 karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Dan majalisar wanda ya kuma kasance shugaban kungiyar kakakin majalisun jiha ta Najeriya, ya sanar da batun sauya shekarsa a yayin shan ruwa na Ramadana wanda Gwamna Bala Mohammed ya shirya, wanda aka yi a gidan gwamnatin Bauchi a daren ranar Asabar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN