Tsabar kishi: Mai gida ya watsa wa matarsa fetur tana barci ya banka mata wuta ya gudu, duba dalili


An zargi wani matashi mai matsakaicin shekaru mai suna Kuryanga da bankawa matarsa ​​Janet John wuta a garin Guyuk da ke karamar hukumar Guyuk a jihar Adamawa

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, majiyar ‘yan uwa ta ce John da Kuryanga sun kawo karshen aurensu na shekaru 7 da suka wuce shekaru 3 da suka wuce, inda kotu ta bayar da umarnin hana shi ganinta saboda mugun halinsa. Kawar John, Noyina, ta ce duk da umarnin kotu na hana shi, Kuryanga ya ci gaba da yi wa Janet barazana.

Yaruwar wacce aka kone mai suna Noyina ta ce Kuryanga ya dauko ‘Premium Motor Spirit’, wanda ake kira da man fetur da ashana, ya sami tsohuwar matarshi tana barci sai ya watsa mata daga bisani ya banka mata wuta.

“Duk da ya auri wata mata tare da hukuncin kotu, har yanzu Kuryanga ya ki sakinta (Yayana, tun a wancan lokacin yana kishi, yana barazana ga rayuwarta da ta masu neman aurenta).

Da dare ya nufi wurin da take kwana a gidanmu, ya zuba man fetur, ya buga ashana ya gudu

An kama Kuryanga kuma ya amsa laifinsa kuma ya roki a yafe mashi. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN