Buhari ya bada izinin fitar da ton 40,000 na hatsi don bikin Easter da Azumi


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin fitar da kayan hatsi ton 40,000 daga rumbun kayan masarufin gwamnati don taimakawa talakawa wajen murnin bikin Easter, azumi da Sallah. Rahotun legit.

Ministan noma da raya karkara, Muhammad Mahmoud, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya bayyana cewa Mahmoud ya gaba da Buhari ne ranar Talata, 12 ga Afrilu, 2022.

A cewarsa, sakin wadannan kayan hatsi zai rage farashin kayan masarufi a kasuwa.

Ya kara da cewa cikin ton 40,000 da za'a saki, za'a baiwa ma'aikatar Hajiya Sadiya Farouq ton 12,000 don rabawa yan gudun hijra dake fadin tarayya.

Yace:

"(Buhari) ya umurceni na fitar da kayan hatsi daga rumbun gwamnati na ma'aikatar noma da raya karkara."

"Za'a yi hakan ne domin rage zafin hauhawan farashin kaya a fadin tarayya. Hakan zai rage farashin kaya don mutane dake shirin Ramadan, Easter da Sallah."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN