An kama wani mai gyaran mota yana balle haƙoran wata gawa domin yin tsafi


Rundunar ‘yan sandan Osun Amotekun ta kama wani ma’aikacin gyaran babbar mota mai shekaru 33 da haihuwa, bisa zarginsa da cire hakoran wata gawa domin yin tsafi samun kudi.

Afeez Odusanya na daga cikin mutane da dama da hukumar ta kama a Osogbo a ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu.

Kwamandan Amotekun, Mista Amitolu Shittu, ya shaida wa manema labarai cewa an gano hakora 12 da ake kyautata zaton an ciro daga gawarwakin da ya tono don yin tsagin samun kudi a hannun wanda ake zargin. 

Ya kuma kara da cewa an kuma gano kashin yatsa biyu daga gare shi.

Shittu ya ce wanda ake zargin yana zaune ne a garin Sagamu da ke jihar Ogun, amma an kama shi ne a wani makabarta da ke garin Ilesa na jihar Osun, yayin da ake zarginsa da tono wata gawa domin yin tsafi.


Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN