Abun kunya bai karewa a fagen siyasar jihar KebbiLokacin yakin neman zabe Yan siyasa kan yi wa talakawa magana da yaren da yawancin talakawan jihar Kebbi ke amfani da shi watau Hausa.

Sai dai bayan darewa kan mulki, sai yan siyasa su rikide karfi da yaji kuma da gangan wajen zama Turawan karfi da yaji.

Shafin labarai na isyaku.com na da tabbataccen hujjar cewa ranar 22 ga watan Mayu 2021 shafin ya sanar da wani babban dan siyasa mai rike da mulki yadda rashin fassara lamurran shugabanci ke nisanta talakawan jihar Kebbi daga fahimtar alkiblar wasu manufofin shugabanci da inda suka nufa.

Sai dai wadannan Yan siyasa sun yi biris da wannan shawara saboda wata akida da manufarsu ta siyasa.

A wannan shekara ta 2022, ba kunya ba tsoron Allah kiri-kiri sai ga wadannan Yan siyasa sun sake fitowa suna yakin neman jama'a ta hanyar yi wa talakawa magana da harshen Hausa koma bayan yaren Turanci da suke yi wajen bayyana ayyukansu ga jama'a. 

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN