Yanzu yanzu: Yan bindiga kimanin 500 sun farmaki garin Kanya a Masarautar Zuru a jihar Kebbi sun kashe soji15


Yan bindiga sun kashe soji 15 da dansandan kwantar da tarzoma guda daya a garin Kanya da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Yan bindiga kimanin su 500 sun farmaki garin kanya, sai dai soji sun fuskance su kuma aka yi mumunar artabu a cikin daren Litinin.

Jami'an soji 15 sun mutu, ana kuma fargaban cewa har da dansandan kwantar da tarzoma guda daya.

Kazalika mun samo cewa Yan bindigan sun tube tufafin sojin da suka kashe suka gudu da su.

Wannan yana zuwa ne bayan Yan bindigan sun kashe Yan sa kai 63 a wani kwanton bauna da suka yi masu ranar Lahadi.

Karin bayani anjima.... 
Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN