Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, akan beli bayan damkeshi daren Alhamis, 17 ga wata.
Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Litinin a Abuja, rahoton TheNation. Bawa yace Obiano na basu hadin kai kan binciken da suke gudanawar kansa.
Babu siyasa cikin wannan bincike. Kun san EFCC, laifuka muke bincike, muna kama wadanda suka aikata laifi sannan mu kaisu kotu."
"Ana zarginmu da tozarta mutane a kafafen yada labarai. Amma zamu cigaba da bincikenmu yadda ya dace."
"An bashi beli kuma muna jiransa ya cika sharrudan belin, yana bamu hadin kai kuma komai na gudana yadda ya dace."
Legit