Fusatattun jama'a sun yi kokarin kone wasu mutane 2 da ransu kan lamarin wata yarinya, duba dalili


Yansandan jihar Oyo sun ceto wasu masu satar mutane "Kidnapers"  yayin da jama'a suka yi kokarin kashe su da duka bisa zargin yunkurin sace wata yarinya a unguwar Alakia-Adelubi da ke birnin Ibadan. Shafin Jaridar isyaku.com ya samo.

Ana zargin cewa Kabiru Salam da Lukman Adisa, sun yi kokarin kwace wata yarinya mai suna Ope, yar shekara 9 daga hannun mahaifiyarta yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wata unguwa ranar Lahadi 2 ga watan Maris.

Kakakin hukumar yansandan jihar Oyo, SP Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin 21 ga watan Maris 2022.

Ya ce isowar yansanda wajen da lamarin ya faru da gaggawa ya yi sanadin ceton mutanen guda biyu bayan jama'a sun kammala shirin kone su da ransu.

Ya ce ana gudanar da bincike a kan lamarin a sashen CID na rundunar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN