Yanzu: Jami'an gidan gyaran hali sun shirya a kotu domin tafiya da Abba Kyari


Labarin da ke iso mu yanzun nan ya bayyana cewa, tuni ma’aikatan gidan gyaran hali na Kuje suka isa babban kotun tarayya, inda ake sauraraan shari'ar Abba Kyari da NDLEA.

Bidioyon da TVC ta yada ya ce, Mista Kyari da sauran jami’an ‘yan sanda za a ajiye su a gidan yari na Kuje, yayin da wanda ake kara na shida da na bakwai za a kai su gidan gyaran hali na Suleja.

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da kai ruwa rana kan batun Abba Kyari da zargin da ake masa tare da wasu jami'ai kan kulla harkallar miyagun kwayoyi.

Kalli bidiyon:

A halin da ake ciki, Mai shari’a Nwite ya ba da umarnin a gaggauta kammala shari’ar wadanda ake kara, kamar yadda ta sanya ranar 28 ga watan Afrilu domin sake duba hujjojin da suka shafi mutum biyu da suka amsa laifinsu a tun farko, inji rahoton Vanguard.

Idan baku manta ba, Umeibe da Ezenwanne; wadanda ake tuhuma na shida da na bakwai a zargin, a ranar 7 ga watan Maris, lokacin da aka gurfanar da su tare da DCP Kyari, sun amsa laifin aikata laifin safarar miyagun kwayoyi da ake tuhumar su da su.

A ranar Litinin din da ta gabata ne kotun ta saurari bahasi daga bangaren masu gabatar da kara da kuma na tsaro, kan bukatar da NDLEA ta gabatar na sake duba hujjojin da ake tuhumar su biyun, domin samun damar yanke musu hukunci daidai da laifinsu.

Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN