Ana maraba da mayaka daga kasashen duniya da ke da sha'awar yaki don kare Ukraine a ci gaba da mamayar da sojojin Rasha ke yiwa kasar a halin yanzu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Volodymyr Zelenskyy, shugaban kasar Ukraine ya rattaba hannu kan wata doka ta wani dan lokaci don tabbatar da faruwar hakan.
Dokar ta dage bukatar takardun shiga kasar ta Ukraine ga duk wani dan kasar waje da ke son shiga rundunar sojin kasa da kasa ta Ukraine, in ji Aljazeera.
Dokar Zelenskyy ta fara aiki ne a ranar Talata kuma za ta ci gaba da aiki muddin dokar soja ta kasance a kasar.
Legit