Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne bayan wani matashin soji da baya sanye da kayan aiki Wanda yake hutun PASS, ya je Unguwar Zuru inda aka sami rashin jituwa tsakaninsa da wani saurayi.
Ya ce sakamakon haka sai sojin ya kira abokansa soji su biyu basa sanye da kayan aiki suka je Unguwar Zuru suka same shi. Ya yi zargin cewa isar su ke da wuya sai suka fara dukan jama'a , lamari da ya sa matasa suka nuna rashin yardarsu ganin cewa sojin sun tayar da hankalin al-ummar Unguwar.
Ya ce sojin ya tafi Barikin soji da ke garin Zuru, daga bisani suka zo da wata mota kirar Hilux da soji hudu masu kakin aiki wasu na dauke da bindiga.
Ya ce sojin sun kama wasu matasa a Unguwar Zuru bayan sojin da ya yi sanadin rigimar ya nuna matasan. Daga bisani sojin sun yi kokarin tafiya da matasan da suka kama zuwa Barikinsu, amma jama'a suka nuna cewa wadanda sojin suka kama ba su cikin wadanda suka sami rashin jituwa da sojin domin sun riga sun gudu kafin isowar sojin.
Ya ce ganin cewa jama'a sun kewaye su ne, sai soji suka yi harbe-harbe da bindiga a cikin iska, sakamakon haka jama'a suka watse.
Wata majiya ta shaida mana cewa sojin sun tafi da matasa da suka kama zuwa Barikinsu domin gudanar da bincike, yayin da wasu gungun mata karkashin wata shugaban mata a Unguwar Zuru suka nufi Fadar Mai Martaba Sarkin Zuru domin su kai koke kan abin da ya faru.
Mun samo cewa ba wanda soji suka harba, kazalika ba wanda suka raunata lokacjn samamen. Sai dai wani ganau ya yi zargin cewa sojin da suka zo da farko su biyu da basu da kakin aiki sun barnata dukiyar jama'a .
Yanzu dai komi ya koma daidai kuma jama'a sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kulllum.