Ku Bani Kuɗi, Ba Kujerar Shugaban Ƙasa Ba, Amaechi Ya Faɗa Wa Magoya Bayansa


Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yayin da ya ke karyata jita-jitar cewa zai fito takarar shugaban kasa a 2023, ya bukaci magoya bayansa su bashi kudi a maimakon kujerar shugabancin kasar.

Idan za a tuna, The Punch ta rahoto cewa wata kungiya, Amaechi Vanguard a Amurka da Canada, ta bukaci jam'iyyar na APC ta zabi Amaechi a matsayin dan takarar jam'iyyar na shugaban kasa a 2023.

A bangarensa, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce zai iya yin takarar shugabancin kasa a 2023 ne, a matsayin shugaban kasa ko mataimaki tare da Amaechi, idan Shugaba Buhari ya dage kan hakan.

Kudi na ke bukata ba kujerar shugaban kasa ba, Amaechi

Amaechi, yayin martaninsa game da bukatar ya fito takarar, ya ce abin da ya ke bukata kawai shine kudi da zai kula da kansa ba shugabancin kasa ba.

Da ya ke magana a Arise TV, ya ce:

"Mutanen da ke son in yi takarar shugabancin kasa a 2023, su bani kudi kawai. Ina bukatar kudi domin in kula da kai na."

Amma, wasu rahotanni sun nuna cewa an ga hotunan takarar shugabancin kasa na Amaechi a wurare da dama a Eagles Square, inda aka yi taron gangamin jam'iyyar APC a ranar Asabar.

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN