Kebbi: Duba abin da matan sojojin da Yan bindiga suka kashe a garin Kanya suka yi a titin garin Zuru (Hotuna)


Matan sojojin da Yan bindiga suka kashe a farmakin garin Kanya a Masarautar Zuru sun gudanar da zanga-zangar lumana a garin Zuru ranar Alhamis 10 ga watan Maris. Shafin labarai isyaku.com ya ruwaito.

Matan sun fara zanga-zangar ne daga kofar shiga Barikin soji na garin Zuru zuwa shingen tsaro na Barikin sojoji da ke kusa da Otal na Mushabida kan hanyar Zuru zuwa Kontagora.

Suna rike da kwalaye suna kiraye-kiraye ga hukumomi kan wasu bukatu da suka rubuta a kwalayen. 

An kula cewa matan suna tafe tare da Yara, wadanda ake zaton yayan wasu sojin da aka kashe ne a farmakin na garin Kanya.

Soji 18 ne suka rasa rayukansu tare da dansanda daya a gumurzun da ya gudana tsakaninsu da Yan bindiga ranar Talata.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN