An gurfanar da wata mata mai suna Zainab Ochero a gaban Kotun Majistare bayan ta cije kunnen saurayinta har kunnen ya gutsire a kasar Kenya. Shafin isyaku.com ya samo.
Rahotanni na cewa takaddama ta taso ne sakamakon jayayya kan kudin hayan babur.
Zainab ta ce saurayinta Joseph Karanja ya bata KSh 100 kudin babur kuma sun yi kadan. Daga bisani cacan baki ya kaure domin shi Joseph ne ya gayyace ta wajen hutawa domin su tattauna matsaloli da ke yawan tasowa a soyayyarsu.
Sai dai lamari ya kazamce bayan sun kasa jituwa a kan samun mafita a lalurar. Lamari da ga kai ga fito na fito tsakaninsu har ta cije shi a kunne kuma kunnen ya gutsire.
Saurayin ta Joseph, ya dauki guntun kunnensa da Zainab ta gutsire ya kai Asibiti ya nemi Likitoci su dinke masa. Sai dai Likitoci sun sanar da shi cewa ko da an dinke kunnen ba zi yi aiki ba.
Yansandan ofishin Kangemi sun gurfanar da Zainab a gaban Kotun Majistare. Alkali Charles Mwanikiya ya bayar da belinta a kan Sh 300.000, kuma za a ci gaba da sauraron shari'ar a wata Maris.
Rubuta ra ayin ka