Da Duminsa: Kotu ta ba da umarnin a saki Matar Abdulmalik Tanko makashin Hanifa


Kotun Majistire dake Kano ta ba da umarnin sakin Jamila Sani, Matar Abdulmalik Tanko, wanda ya amsa kashe Hanifa Abubakar a Kano
.

Daily Trust ta rahoto cewa Matar, wacce ake zargi da haɗa baki da maigidanta wajen sace Hanifa da kashe ta, ta samu yanci ranar Jumu'a.

Jamila ta bayyana gaskiyar lamari, lokacin da ta ba da shaida kan mijinta a babbar Kotun jihar Kano, ranar Alhamis.

Tun da farko dai lauyan jiha, Barista Lamido Soron Dinki, ya roki Kotu ta duba shaidar da matar ba bayar kan mijinta.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda Matar Tanko, Jamila Muhammad Sani, ta yi bayani dalla-dalla a gaban Kotu kan abinda ta sani game da kisan Hanifa.

Matar ta shaida wa Alkali duk abin da ya faru tun daga ranar da Tanko ya zo da yarinyar ƙarama gidanta, har zuwa ranar da ya ɗauke ta da daddare.

Abin da Jamila ta faɗa wa Kotu

Wani sashin bayaninta, Matar Tanko ta ce:

"Ya kawo yarinyar gidana, ya faɗa mun mahaifiyarta malama ce a makarantarsa, ta samu aiki a Saudiyya dan haka zata je Abuja ta sanya hannu a wasu takardun tafiya."

"Ta kara kwana biyu, sai ce mun ya yi ta kira shi wai kuɗi sun kare mata a Kaduna. Daga nan na daina tambayarsa saboda ya ce ba ta da kuɗin dawowa."

"Bayan kwana 5 yace zai kaita gida, lokacin da daddare ne, na ɗauki kayan makarantarta na bashi, kawayenta na bacci lokacin. Na nemi ya bari sai da safe saboda suna bacci amma ya matsa."

A zaman cigaba da sauraron ƙara kan kisan Hanifa Abubakar, gwamnatin Kano ta fara gabatar da shaidu.

A ranar Laraba, Shaidu uku da aka gabatar sun mika wa Kotu abubuwa 10 da suka kwato a hannun waɗan da ake zargi.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN