Bello Turji ya banbanta kansu da yan Boko Haram, ya ce basu da wata akida, duba saura


Barandanci, ta'addanci, garkuwa da mutane sun zama ruwan dare a Arewacin Najeriya musamman yankin Arewa maso yamma.

Jihohin dake fama da matsalar yan bindiga sun hada da Zamfara, Katsina, Sokoto, Kaduna, da Neja.

A jihar Zamfara kadai, an raba mutane akalla 785,000 da muhallansu.

Tashar Trust TV ta zanta da kasurgumin jagoran yan bindiga Bello Turji, inda ya bayyana cewa ba shi da alaka da yan Boko Haram.

A cewarsa, su basu da wata akida ko ra'ayiin siyasa. Kawai su dau makami ne don kare kawunansu.

A cewarsa:

"Bamu da ra'ayin kafa wata kungiyar addini. Bamu da niyyar yanke wata kasa, kuma babu ruwanmu da siyasa. Mun dau makami ne don kare rayukan al'ummarmu dake kashewa."

"Ba wai bamu da imani bane ko bamu da tsoron Allah ba."

Mutane sun yi mamakin yadda na zama dan bindiga, ni makiyayi ne: Bello Turji

Turji, wanda dan asalin garin Fakai a karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara ne, ya bayyana cewa wadanda suka san shi sun yi mamakin yadda ya fara sata da kashe-kashe.

Turji ya kara da cewa a rana guda aka kashe masa yan uwa shida bayan sacewa iyayensa Shanu sama da dubu.

Haka yasa ya dau bindiga don kare hakkin Fulani yan uwansa da aka takurwa a karamar hukumar Shinkafi ta jihar.

Amma bisa harkokin kashe-kashe da ya dau alhaki, mutane da dama da basu da hula da gwamnatin sun rasa ayukansu da rayukan yan uwansu sakamakon hare-harensa.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN