Uwargida da dangin amarya sun ba hammata iska a filin biki, ango ma ya sha matsa


Wani abun al'ajabi ya faru a wajen wani biki, yayin da taron ya koma filin daga sakamakon fada da ya kaure a tsakanin uwargida da ta je taya mijinta murna da dangin amarya.

Kamar yadda shafin Northern habiscus ta wallafa a Instagram, rikicin ya samo asali ne a yayin da ake shirin daukar hoto tsakanin mijin da uwargidarsa.

Ita uwargidan ta yi kokarin nuna ita ke da miji don haka ta dare cinyarsa ta zauna domin su dauki hoto, inda hakan bai yiwa angon dadi ba har ta kai ya tureta.

Wannan ya fusata uwargidar wacce ta fadi a kasa warwas, kuma a kokarinta da tashi daga faduwar da ta yi sai ta bige amarya bisa kuskure. Lamarin da ya sa dangin amarya ramawa.

An tattaro cewa a lokacin da dangin amaryar suka far mata, sai da suka yayyaga mata riga. Wannan bidirin dai duk ya faru ne a garin Minna, babbar birnin jihar Neja.

A bidiyon wanda ke yawo yanzu a shafukan soshiyal midiya, an gano inda aka shake shi kansa angon.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN