Na so yin shuhura da sunan karuwa a Twitter, Sabuwar Salma ta Kwana Casa'in


Sabuwar Salma ta shirin Kwana Casa'in ta sanar da dalilin da ya hana ta shahara a dandalin sada zumunta na Twitter wanda ta bayyana shafin ta na Instagram.

A wata wallafar bidiyo da ta yi, ta yi bayani cikin harshen turanci.

A bayanin sabuwar Salma, ta ce tun bayan dawowar Twitter a Najeriya ta ga yadda ake shiga jerin batutuwa wadanda suka fi shahara da ake tattaunawa a dandalin wato trending news.

Cikin kankanin lokaci za ka iya samun masu sake wallafa hotuna ko batutuwan ka a dandalin, hakan yasa ta so amfani da wani likau, wanda ake kira da Hashtag na Ashawo wanda karuwa ya ke nufi a jikin hotunan ta da rubutun ta.

Ta kara da cewa:

"Na tuna daga yankin arewa nake shiyasa na hakura don a zauna lafiya. Shiyasa na kasa amfani da likau din wanda da na yi amfanin da shi ranar da tawa ta kare."

Me masu tsokaci suka ce?

Nan take jama'a suka yi caa a kan sabuwar Salman inda suka ce gara da ta fasa dan kuwa sai an yi maganar.

Wadanda ba Hausawa ba 'yan arewa sun dinga kushe wannan abu da suka kira da rashin 'yanci yayin da Hausawa suka dinga soka wa jarumar maganganu marasa dadi.

Bidiyon jarumar ya tabbatar da cewa, ba don tsoron cece-kuce a shafukan sada zumunta ba, da wani abun ido ba zai iya kallo ba.

Ga bidiyon jarumar:

A kwanaki biyu da suka gabata, jaruma Rahama Sadau ta wallafa wasu hotunan ta sanye da wata bakar riga wacce ke bayyana ilahirin surar jikin ta.

Kamar yadda ta wallafa a shafin ta mai suna @rahamasadau, ta saka hotunan tare da rubuta:

"Ba za ka taba gajiya ba matukar ka na gwada sabbin abubuwa".

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN