Kungiyar masu magungunan gargajiya na kasa reshen jihar Kebbi ta dage taron zaben shugabanninta (Hotuna)


Kungiyar masu sayar da maganin gargajiya na Najeriya, National Association of Traditional Medicine Practitioners of Nigeria NANTMP reshen jihar Kebbi, ta dage babban taronta na zaben shugabannin jihar Kebbi har ranar 15 ga watan Mayu 2022.

Jaridar isyaku.com ya samo haka yayin zantawa da Kakakin kungiyar na kasa PRO Alhaji Ibrahim Agaie.

Mun samo cewa an dage taron zaben sabbin shugabannin ne sakamakon wasu dalilai na cikin gida.

An nada Yusuf Abubakar Argungu a matsayin shugaban rikon kwarya na kungiyar a halin yanzu.

'Yaan kungiyar maza da mata daga sassan jihar Kebbi ne suka sami halartar taron wanda aka gudanar a garin Birnin kebbi ranar Litinin 15 ga watan Fabrairu 2022.
Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN