Yanzu-yanzu: Za a mika wa kasar Amurka Abba Kyari bayan kammala binciken NDLEA inji majiyar fadar shugaban kasa, duba dalili


Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce akwai yiwuwar za a mika dakataccen Mataimakin Kwamishinan yansanda Abba Kyari ga mahukuntar kasar Amurka bayan kammala bincike kan tuhumar da ake masa kan badakalar kasancewa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi.

Jaridar The Nation ta ce hukumar NDLEA ta cafke Abba Kyari tare da wasu yansanda hudu kan hannu a safarar miyagun kwayoyi ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu kuma tana gudanar da bincike. 

Ta ce Gwamnatin tarayya ta kammala shirin mika Kyari zuwa kasar Amurka inda ake nemansa ruwa a jallo bisa zargin alaka da fitaccen dan damfara Ramon Olorunwa Abbas, Wanda aka fi sani da suna Hushpuppi, kan zambar dala miliyan $1.1.

Kazalika The Nation ta ce an dauki tsawon kwanaki hudu mahukuntan yansanda na jan kafa kuma sai da fadar shugaban kasa ta ba Safeto janar na yansanda Baba Usman umarni cewa yansanda su mika kyari ga hukumar NDLEA domin fuskantar bincike. 

Kafin yansanda su mika Kyari, tun farko hukumar NDLEA ta saki wani faifen bidiyo da ke nuna yadda Abba Kyari ke kokarin aikata ba daidai ba ta hanyar yin amfani da matsayinsa.

Wata majiya ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya karbi wani rahotu kan Abba Kyari daga wajen shugaban hukumar NDLEA Janar Buba Marwa mai murabus.

Wasu daga cikin yansanda da aka kama tare da Abba Kyari sun hada da Mataimakin Kwamishinan yansanda Sunday Ubuah (ACP), Bawa James, mai mukamin Assistant Superintendent of Police (ASP); sai kuma Inspector Simon Agrigba da Inspector John Nuhu.

Wata majiya a fadar shugaban kasa ta ce yanzu haka Najeriya na kammala cika ka'idoji da yarjejeniyar Mutual Legal Assistance Treaty (MLAT) tare da kasar Amurka kan lamarin mika mata Abba Kyari. 

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN