Hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin NBC ta dakatad da haska shirin Idon Mikiya na tashar VisionFM kan laifin tattauna tsawaita nadin shugaban hukumar leken asirin kasa NIA, Rufa'i Abubakar.
A wasikar da NBC ta turawa shugaban tashar VisionFM ranar Laraba, tace ta sanyawa gidan rediyon takunkumi ne saboda illar maganganun da sukayi a shirin 'Idon Mikiya' a ranar 5 ga Junairu, 2022.
NBC tace wannan ya sabawa sashe 39 (3) (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya da ta haramta tattauna lamuran tsaro da hukumominta.
A cewar wasika:
"Abubuwan da kuke tattaunawa, ciki har da nadi a hukumar leken asirin Najeriya (NIA) ya sabawa sashe 39 (3) (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya sanya takunkumi kan abubuwan da suka shafi lamuran tsaro."
Hukumar ta ci Vision FM tarar N5 million kuma ta dakatad da shirin Idon Mikiya na tsawon watanni shida.
NBC tace ana bayyana sirrukan gwamnati a shirin kuma hakan na da illa da tsaro.
A watan Disamba, shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita wa'adin shugaban NIA duk da cece-kucen da akeyi.
Legit Hausa
================
Daga Jaridar iyaku.com
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook fFacebook.com/isyakalabari