Da duminsa: Duba Jiga-jigan da suka yi nasara da wadanda suka sha kasa yayin da APC ta nada shugabanni


A yau Alhamis, 2 ga watan Fubrairu 2022 ake rantsar da shugabannin APC na reshen jihohi. Punch ta ce wadanda ke tare da gwamnoni sun yi galaba.

Wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar APC mai mulki da suka rasa ikon jam’iyya a hannun gwamnonin jihohinsu sun hada da wasu Ministoci na tarayya.

Daga cikin Ministocin akwai Rauf Aregbesola, Festus Keyamo SAN da kuma Alhaji Lai Mohammed.

Tsofaffin gwamnoni kamar su Ibikunle Amosun da Abdulaziz Yari da kuma su Sanata Kabiru Marafa sun gaza karbe jam’iyya daga hannun abokan fadansu.

Har zuwa dazu a jihohi irinsu Osun, shugaban ‘yan taware na APC, Alhaji Rasaq Salinsile ya ce babu tabbacin wani bangare na shugabannin za a rantsar a yau.

Shugaban APC na Osun, Prince Gboyega Famoodun wanda yake tare da gwamnatin Gboyega Oyetola ya ce babu tababa a kan cewa su za su rike jam’iyyar APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jiga-jigan APC

Shugaban APC na rikon kwarya Hoto: nationaldailyng.com Source: UGC

A jihar Kwara, shugabannin ‘yan taware na APC ba su san da bikin rantsar da shugabannin jihohi ba. Amma kuma an gayyaci mutanen Prince Sunday Fagbemi.

Bayan Kwara da Osun, a Ogun ma da alamun cewa sakatariyar APC za ta rantsar da bangaren Yemi Sanusi ne, tayi watsi da ‘yan tawaren da ke tare da Amosun.

'Yan siyasan Zamfara sun sha kashi

Rahoton ya ce a Zamfara an yi fatali da 'yan tsagin Kabiru Marafa da na Abdul’Aziz Yari yayin da uwar jam’iyya ta tafi da mutanen da ke tare da gwamna Matawalle.

Rikicin gidan APC tsakanin Ovie Omo-Agege da Keyamo ya ki karewa a Delta, inda aka zabi a rantsar da Omens Sobotie a matsayin shugaban jam’iyya na jiha.

A Bauchi, mutanen Adamu Adamu za a rantsar, hakan ya na nufin babu labarinsu Yusuf Tugar. Kawo yanzu babu labarin wanda aka zaba tsakanin tsagogin Kano.

Inda ake ta rikici

Jihohin da ake samun sabani tsakanin Gwamnoni da sn manyan jam’iyya sun kunshi: Osun, Ogun, Kwara, Kebbi, Kano, Delta, A/Ibom, Rivers, Bauchi da Zamfara.

Ku na da labari cewa tsohon ‘dan majalisar Kaura Namoda/Birnin Magaji, Aminu Sani Jaji ya caccaki Alhaji Abdulaziz Yari, ya ce ba a san da zamansa a jam'iyya ba.

Source: Legit.ng

================

Daga Jaridar iyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook fFacebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN