Da duminsa: An yaga postocin yan takarar jam'iyun adawa a garin Birnin kebbi gabanin zaben kananan hukumomi a jihar Kebbi


Wasu da ba a san ko su waye ba, sun yaga postocin takara na jam'iyyun adawa gabanin zaben kananan hukumomi a jihar Kebbi.

Jaridar isyaku.com ya lura an yaga postocin yan takarar ne daga shataletalen Haliru Abdu zuwa titin Ahmadu Bello har zuwa shataletalen Asibitin Sir Yahaya a garin Birnin kebbi.

Sai dai rahotanni na cewa har zuwa titin Sarki Haruna da sauran sassan garin Birnin kebbi an yaga postocin.

Bincike da Jaridar isyaku.com ya gudanar, ya nuna ba hannun wata hukuma dangane da cire, yaga, ko lalata postocin yan takara na kowane irin jam'iyar siyasa a jihar Kebbi.

Sai dai wata majiya da ke da masaniya kan harkoki da halayen yan siyasa a jihar Kebbi, ya yi hasashen cewa ba mamaki yan daban siyasa na yan siyasa da ke kira da manuniya cewa a yi tashin hankali ne ke sa yan daban siyasa su aikata wannan aiki.

Isah Asalafi, Kakakin jam'iyar siyasa na jam'iyar APC reshen jihar Kebbi tsagin Gwamna Bagudu, ya ce bai da labarin aukuwar hakan a lokacin da muka tuntube shi kan lamarin.

Kazalika Umar Namashaya Diggi, Sakataren jam'iyyar APC Asali, tsagin tsohon Gwamna Adamu Aliero, ya ce basu da hannu wajen wannan aiki. Ya ce "A ko yaushe mu muna kira ne ga magoya bayan mu cewa a zauna lafiya"

================

Daga Jaridar iyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook fFacebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN