Da Duminsa: Miyagu sun halaka mataimakin kwamishinan yan sanda, duba ka gani


Mazauna yankin Agwa clan dake karamar hukumar Oguta, jihar Imo sun shiga jimami biyo bayan kisan gillan da akai wa mataimakin kwamishinan yan sanda mai ritaya kuma lauya, Barista Christian Kpatuma.

The Nation ta tattaro cewa marigayi mataimakin kwamishina (ACP) wanda aka fi sani da "Hippies" ana zargin ya rasa ransa ne a hannun wasu yan kungiyar asiri.

Rahotanni sun nuna cewa yan kungiyar asirin waɗan da sanannu ne a yankin Agwa, sun je har cikin gidansa da safiyar Laraba, kuma suka kashe shi.

Wani sanannen mutumi a yankin da abun ya faru, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya roki gwamna Hope Uzodinma, na jihar Imo ya yi duk me yuwu wa wajen hukunta waɗan da suka kashe marigayi ACP.

Mutumin yace:

"Ina kira ga mai girma gwamna ya jibge jami'an tsaro a Agwa da nufin su farauto waɗan nan yan ƙungiyar asirin da mutanen da suka ɗauki nauyin su, har sai an hukunta su."
"Mutanen Agwa na rayuwa cikin fargaba, duk da 'ya'yan yankin ne suka kafa Hedkwatar yan sanda (wacce ake alfahari da ita a jihar Imo), kwana uku kacal da ƙaddamar da ita, tare da Yan Bijilanti. Gaskiya ina cikin takaici."

Shin hukumar yan sanda ta samu rahoto?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo, CSP Michael Abattam, yace ya ji labarin faruwar lamarin, amma har yanzun bai samu bayani a hukumance daga DPO na yankin ba.

"Na ji labarin abin da ya auku, amma ina son samun bayanai a hukumance daga DPO na yamkin, kafin na dawo gare ku."

A wani labarin na daban kuma Ɗan Sarauniya zai ƙara kwana a gidan gyaran hali saboda shari'ar Sheikh Abduljabbar

Kotu ta ɗage sauraron karar tsohon kwamishinan ayyuka na Kano, Muazu Magaji saboda ta yi karo da shari'ar Sheikh Abduljabbar.

A halin yanzun an ɗage ta Ɗan sarauniya zuwa 4 ga watan Fabrairu, 2022, yayin ta Malam Abduljabbar zata wakana 3 ga watan Fabrairu.

Source: Legit.ng

================

Daga Jaridar iyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook fFacebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN