Cutar Sikila: Abubuwa bakwai da ya kamata ku sani game da cutar


Cutar sikila ko amosanin jini na daya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS.

Larurar amosanin jini, wato sickle cell anaemia, mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al'umma baki daya.

An ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar yaki da cutar amosanin jini wato sikila a duniya. Rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakar da al'umma kan wannan cutar a matakin kasa da kuma na kasa da kasa.

Kan haka ne BBC ta yi nazari kan wasu abubuwa bakwai dangane da cutar:

1. Najeriya ta fi yawan masu cutar a duniya

Bincike ya nuna cewa duk shekara ana haifar jarirai 300,000 a duniya kuma rabi daga wannan yawan a Najeriya ake haifar su. Daga cikin 150,000 na Najeriya din nan 100,000 ne ke mutuwa duk shekara.

Alkaluma sun nuna cewa mafi yawan masu cutar suna arewacin kasar ne. Masana kiwon lafiya sun yi amanna cewar rashin yin gwajin jini kafin aure yana taka rawa sosai wajen haifar yara masu dauke da cutar sikila a kasar.

2. Shan magunguna har abada

Masu fama da cutar sikila suna fara shan wasu magunguna tun daga lokacin da aka gano suna dauke da cutar har zuwa karshen rayuwarsu, kamar yadda Dr Bashir Isa Waziri, wani likita a asibitin koyarwa na Aminu Kano ya shaida mana.

''Daga cikin magungunan akwai 'Folic Acid' wanda yake kara musu jini, saboda kwayoyin jininsu na yawan karewa. Akwa kuma 'Paludrine' magani ne da ke kare su daga kamuwa da cutar maleriya don tana wahalarsu sosai idan suka kamu.

Sai maganin 'Peniciillin V' shi kuma aikinsa shi ne kare su daga cututtuka masu alaka da numfashi. Sai 'Hydroxyurea' wanda yake taimaka wa kwayoyin jinin siffarsu ta zama mai kyau, yake kuma taimaka musu wajen rage tashin ciwon. Amma yawanci shi sai wanda ciwon ke masa tsanani,'' in ji likitan

3. Yawaita shan ruwa

Yawan shan ruwa abu ne mai matukar muhimmanci ga masu cutar sikila saboda rashin ruwa yana tayar musu da ciwon kwankwaso da na gabobi.

Sannan shan ruwan na sa jini ya dinga gudu yadda ya kamata kuma kwayoyin jini su dinga wucewa cikin jiyoyi, wanda haka ke hana ciwon yawan tashi.

4. Zafin ciwon ya fi na nakuda

Tsananin zafin ciwon kwankwaso da masu cutar kan yi fama da shi lokaci zuwa lokaci yana matukar uzzura musu. Kwararru a harkar lafiya sun ce zafinsa ya fi na nakuda.

Dr Bashir Waziri ya ce: "Suna jin ciwon kashi kamar ana kwankwatsa shi, jini ba ya isa wasu wuraren don haka idan suka taru a waje daya sai su saka ciwo.''

5. Shafar lafiya jima'i

Likitan ya kuma cewa wannan ciwo bai bar masu shi ta bangaren shafar lafiyar jima'insu ba. Ciwo ne da ke hana su rawar gaban hantsi sosai a wasu lokutan ta wannan fanni.

''Ga maza dai yawanci gbansu ya kan mike mike ya ki sauka, kwayoyin jini masu kamar kauje na makalewa a gabansu sai jinin ya ki fita ya taru a wajen, sai al'aurarsu ta mike ta ki sauka.

''A wasu lokutan har sai an yi 'yar karamar tiyata, wasu kuma da an sanya kankara sai ta taimaka wajen kwantar da gaban,'' in ji Dr Bashir.

6. Kuka da ihu ba babba ba yaro

Tsananin zafin da ciwon ke zuwa da shi kan sa masu yin sa su dinga gurzar kuka tare da gunji da gurnani. A irin wannan yanayi ba babba ba yaro za a ga sun fita hayyancinsu.

Wata mai fama da wannan lalura da ba ta so a fadi sunanta ta ce: ''Ba zan iya kwatanta yadda xiwon yake ba, illa iyaka zan ce na kan ji kamar an kwankwatsa min kashina da guduma. Shi ya sa duk dauriyar mutum dai an ji sautin kukansa.'

'7. Karaya ba tare da jin ciwo ba

Dr Bashir ya ce daga cikin wasu abubuwan mamaki dangane da wannan ciwo shi ne yadda a wasu lokutan sai ƙashin wata gaɓa ta jikin masu ciwon ya karye ɓal.

''Ba komai ke jawo hakan ba sai tsabar zafin ciwon da ke taso musu,'' in ji shi.

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN