Abin da ya kamata ku sani kan sabuwar dokar zabe da Buhari ya sanya wa hannu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta kasar wadda aka dauki tsawon lokaci ana ka-ce-na-ce a kai.

Buhari ya saka hannu kan dokar ne ranar Juma'a a yayin wani takaitaccen buki a fadarsa a gaban idon Shugaban majalisar dattawa da na majalisar wakilan kasar.

Da yake jawabi lokacin da yake sanya hannu kan dokar, shugaban ya bukaci 'yan majalisar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramta wa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri'a a zaben shugabannin jam'iyya ko kuma na 'yan takara.

Shugaban ya ce wannan sabuwar dokar zaɓen, za ta ƙara inganta harkar zaɓe ta hanyar tabbatar da an yi abubuwa a bayyane ba tare da nuƙu-nuƙu ba a lokacin zaɓen da kuma rage abubuwan da za su ja ƴan takara su yi ta ƙorafe-ƙorafe.

Shugaba Buharin ya bayyana cewa wannan ƙoƙarin na sa hannu kan dokar zaɓen na daga cikin tsare-tsaren gwamnatinsu na ƙara buɗe hanya domin gudanar da sahihin zaɓe mai inganci.

Ya kuma ce babu wani mai riƙe da muƙamin siyasa da zai iya zama wakilin masu zaɓe wato 'dalaget-dalaget' ko kuma a zaɓe shi a yayin babban taron jam'iyya domin ya tsaya takarar zaɓe.

Da yake jawabi yayin zaman saka wa dokar hannu, Shugaba Buharin ya ce kudurin dokar na yanzu da aka yi wa gyara ya fi inganci sosai da wanda aka fara kawo masa.

"Akwai wasu muhimman tanade-tanade a wannan dokar da za su kawo sauye-sauye masu alfanu a tsarin zaben a Najeriya ta hanyar fito da salon amfani da naurori wanda zai tabbatar kowane dan kasar yancinsa na ya jefa kuma ta yi tasiri.

"Haka ma dokar za ta tabbatar yin komai a bayyane, bisa ƙa'ida da bin gaskiya kuma da rage yawan ƙorafe-ƙorafe da ƙararrakin da 'yan takara da jam'iyyu ke shigarwa a duk lokacin da aka yi zabe.

"Wannan namijin ƙoƙarin ya zo daidai da manufarmu ta samar da wani tsarin doka da zai ba da damar yin zabe mai inganci da kowa zai yi alfahari da shi," in ji shugaban ƙasar.Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta kasar wadda aka dauki tsawon lokaci ana ka-ce-na-ce a kai.

Buhari ya saka hannu kan dokar ne ranar Juma'a a yayin wani takaitaccen buki a fadarsa a gaban idon Shugaban majalisar dattawa da na majalisar wakilan kasar.

Da yake jawabi lokacin da yake sanya hannu kan dokar, shugaban ya bukaci 'yan majalisar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramta wa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri'a a zaben shugabannin jam'iyya ko kuma na 'yan takara.

Shugaban ya ce wannan sabuwar dokar zaɓen, za ta ƙara inganta harkar zaɓe ta hanyar tabbatar da an yi abubuwa a bayyane ba tare da nuƙu-nuƙu ba a lokacin zaɓen da kuma rage abubuwan da za su ja ƴan takara su yi ta ƙorafe-ƙorafe.

Shugaba Buharin ya bayyana cewa wannan ƙoƙarin na sa hannu kan dokar zaɓen na daga cikin tsare-tsaren gwamnatinsu na ƙara buɗe hanya domin gudanar da sahihin zaɓe mai inganci.

Ya kuma ce babu wani mai riƙe da muƙamin siyasa da zai iya zama wakilin masu zaɓe wato 'dalaget-dalaget' ko kuma a zaɓe shi a yayin babban taron jam'iyya domin ya tsaya takarar zaɓe.

Da yake jawabi yayin zaman saka wa dokar hannu, Shugaba Buharin ya ce kudurin dokar na yanzu da aka yi wa gyara ya fi inganci sosai da wanda aka fara kawo masa.

"Akwai wasu muhimman tanade-tanade a wannan dokar da za su kawo sauye-sauye masu alfanu a tsarin zaben a Najeriya ta hanyar fito da salon amfani da naurori wanda zai tabbatar kowane dan kasar yancinsa na ya jefa kuma ta yi tasiri.

"Haka ma dokar za ta tabbatar yin komai a bayyane, bisa ƙa'ida da bin gaskiya kuma da rage yawan ƙorafe-ƙorafe da ƙararrakin da 'yan takara da jam'iyyu ke shigarwa a duk lokacin da aka yi zabe.

"Wannan namijin ƙoƙarin ya zo daidai da manufarmu ta samar da wani tsarin doka da zai ba da damar yin zabe mai inganci da kowa zai yi alfahari da shi," in ji shugaban ƙasar.

Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan ya yi karin bayani kan yadda dokar za ta inganta zabe a Najeriya.

"Wannan doka an kawo ci gaba a ciki wanda INEC za ta iya amfani da damarmaki da take da su ta hanyar fasaha wanda zai rage maguɗi ko kuma aringizo da kuma ɓata zaɓe da kansa.

A cikin wannan sabuwar doka da shugaban ƙasa ya sa wa hannu yau ya ba da wasu hukunci masu tsanani na yadda duk wanda aka kama yana ƙoƙarin ya ɓata zaɓe to za a ɗaure shi ko kuma ya boya tara mai nauyi wadda wannan muna ganin zai iya inganta aikin zaɓen kansa.

"Kuma abin da nake fata a nan shi ne, ita hukumar zaɓe ta yi amfani da damarmaki da aka ba ta, mu kuma ƴn siyasa mu tabbatar da cewa ba mu yi ƙoƙarin yi wa dokokin da aka kawo karan-tsaye ba.

Sai dai kuma har yanzu ga alamu da sauran rina a kaba domin shugaban ya bukaci Æ´an majalisar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramta wa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri'a a zaben shugabannin jam'iyyu ko kuma na 'yan takara wanda in ji shi haka ya saba wa kundin tsarin mulki.

Ko wannan na nufi sai an sake maido wa shugaban kasar da dokar bayan yin wannan gyara? Tambayar kenan da BBC ta yi wa Malam Garba Shehu mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar.

"Daga yanzu ta zama doka, babu wani tababa a kan wannan. Amma dai maimakon a sake riƙe ta a ce a koma baya, ya nemi cewa su koma su warware wannan matsala don ya saɓa da tsarin mulki na Najeriya.

"DUk abin da suka yi idan shugaban ƙsa bai sa hannu a kai ba to bai zama doka ba, saboda haka zai sa hannu akai.

"Kuma in yau aka kira babban taro na jam'iyya, waɗannan jami'an da aka ce an ɗauke musu damar jefa ƙuri'a a zaɓen tarurruka na jam'iyya ba za su jefa ƙuri'a ba har sai an yi gyara ga wannan doka.

Sai dai wannan na nufin wannan dokar zaɓen daga yanzu ta fara aiki, kuma ta maye gurbin dokar zaɓen da ƙasar ke amfani da ita a tsawon shekaru 12, wadda aka kafa a shekarar 2010.

BBC 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN