Bayan yi wa bayin Allah kisar gilla a kauyen Zamfara, yan bindiga sun kuma hana a yi masu Jana'iza , duba ka gani


Kwanaki hudu da kashe mutane akalla 12 a kauyen Daraga, mutanen wannan gari a jihar Zamfara sun ce ‘yan fashin daji sun hana ayi masu sutura.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto inda aka ji al’ummar kauyen Daraga a karamar hukumar Maru su na kokawa a game da halin rashin tsaron da suke ciki.

Mutanen da ke zama a yankin sun shaidawa BBC Hausa cewa sun gagara birne ‘yanuwansa da aka hallaka saboda har yanzu ‘yan bindiga sun ki barin garinsu.

Wani mutumi da ya zanta da manema labarai ba tare da ya bari an kama sunansa ba, ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun kona gidansa, sun bindige mutanensa.

Baya ga ‘danuwansa da aka kashe, wannan mutum ya ce ‘yan bindigan sun harbe ubangidansa a shago.

Halin da mutane su ke ciki

“Yanzu haka da na ke yi maka magana, babu mutum ko daya a wannan kauyen. Dukkanmu mun tsere daga yankin.”

“An tabbatar da cewa an kashe mutane 12, sannan da-dama sun samu rauni a harin. An kashe mani abokai takwas.”

“Kuma ‘yan bindigan su na nan a kewayen karkarar, sun hana mu dauko gawarsu, mu yi masu suturam a birne su.”

- Inji majiyar

Ina jami'an tsaro?

Wannan Bawan Allah ya shaida cewa sun yi kokarin tuntubar jami’an tsaro, amma ba a dace ba. A cewarsa ‘yan bindigan sun fi karfin dakarun da su ke Dan Kurmi.

Majiyar ta ce jama’a sun tsere daga kauyukan Dan Kurmi, Bena, Zargado a jihar Zamfara, haka zalika duk an yi kaura daga yankunan Wasagu da Unashi a Kebbi.

Da aka nemi a tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai dauki waya ba.

Siyasar Zamfara

A Zamfara ta siyasa ake yi, inda kwanaki aka ji tsohon ‘dan majalisar Kaura Namoda/Birnin Magaji, Aminu Sani Jaji ya caccaki tsohon gwamna, Abdulaziz Yari

Hon. Aminu Sani Jaji ya bi gwamna mai-ci Bello Matawalle wanda aka damkawa APC, kuma ya ce bai tunanin har yanzu Yari yana da rajistar zama ‘dan jam’iyya.

Source: Legit.ng

================

Daga Jaridar isyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook Facebook.com/isyakulabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN