Balaguron uwargidan shugaba Buhari a cikin iirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja, abin da ya faru


Uwargidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari ta yi balaguro cikin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja ranar Alhamis 10 ga watan Fabrairu. Jaridar isyaku.com ya samo.

Aisha Buhari ta ziyarci jihar Kano ne domin tabbatar da ganin cewa an yi wa Hanifa Abubakar adalci bayan an yi mata kisar gilla a Kano. 

Mataimakan Aisha kan harkar labarai sun wallafa hotunanta lokacin da take shiga jirgin sama daga Kano zuwa Kaduna.

Kazalika sun wallafa hotunanta lokacin da ta shiga jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja.

An gano jami'an tsaro na soji da DSS a karshen yankin taragon da Aisha ke ciki tare da kaninta Mahmud Ahmad da sauran mataimakanta.


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN