Yanzu-yanzu: Gwarazan yansanda sun aika wasu miyagu lahira da gaggawa a jihar Arewa, duba dalili


Rahotanni daga jihar Katsina na cewa Gwarazan yan sanda sun samu nasarar daƙile wani kazamin harin yan bindiga da suka addabi jihar, sun sheke guda 5 sun kwato mutanen da aka sace da dabbobi
.

Vanguard ta rahoto cewa yan bindigan sun yi yunkurin kai hari kauyukan Kuru da Dangani a karamar hukumar Musawa jihar Katsina.

Sauran abubuwan da yan sandan suka kwato sun haÉ—a da, bindiga kirar AK-47 guda É—aya da zaren alburusai da kuma Mota kirar Gulf III.

Yan sanda

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Katsina, SP Gambo Isa, shi ne ya bayyana haka yayin da yake nuna wa manema labarai wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato a Hedkwatarsu ranar Jumu'a.

Gambo ya yi bayanin cewa kwamandan yan sanda na yankin Dutsinma ya samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar 10 ga watan Janairu, cewa yan ta'adda da yawa sun farmaki yankin Musawa.

Nan take ya jagoranci tawagar yan sanda zuwa hanyar da ake tsammanin zasu biyo kusa da kauyen Dangani, suka yi kazamin artabu, yan sanda suka kashe yan ta'adda 5, suka kwato makamai.

Wani harin na daban

SP Gambo ya ce:

"A wannan rana dai da misalin karfe 4:00 na Asuba aka sake kiran kwamandan Dutsinma, nan take ya sake haÉ—a tawaga suka fukanci wata tawagar yan bindiga kusa da kauyen Dangani, duk a Musawa."

"Lokacin yan bindigan sun sato wani dattijo, Alhaji Sule, daga kauyen ÆŠankwari a cikin wata farar mota Gulf III, mai lambar rijista BKR 367 XA."

"Kwamandan da yan tawagarsa suka ja daga da yan bindiga, aka cigaba da artabu, wanda ya tilasta musu tserewa suka bar mutumin da kuma motar anan wurin.

Ma'aikacin gwamnatin jihar Sokoto, Ladan Ibrahim, na ɗaya daga cikin mutum 45 da aka damƙe kan zargin taimakawa Boko Haram da kuɗaɗe.

Iyalan Malam Ibrahim sun bayyana halin da suka tsinci kan su tun bayan kama jigon da yake É—aukar nauyin su baki É—aya.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN