Allahu Akbar: Yadda yunkurin ISWAP na hadewa da Boko Haram ya ci tura


Yunkurin kungiyar ta'addanci ta Islamic State West Africa Province (ISWAP) na hadewa da kungiyar Boko Haram bayan ta fada wa kungiyar a dajin Sambisa ya tashi a tutar babu, kamar yadda bayanin rahoton majalisar tsaro na majalisar dinkin duniya ya bayyana.

Jaridar HumAngle ta ruwaito cewa, kungiyar ISWAP ta so hadewa da mayakan Boko Haram amma hakan ya gagara kamar yadda kungiyar kiyasi ta sanar a rahoton ta na 29 kan IS da Al-Qaeda.

Rahoton da aka mika wa kwamitin majalisar tsaro na majalisar dinkin ya kara da bayyana cewa:

"Kungiyar ISWAP da mayakanta 4,000 zuwa 5,000 sun sake shirya kansu zuwa yankuna hudu. Yankin tafkin Chadi, Tumbuna, dajin Sambissa da Timbuktu."

Rahoton ya kara da cewa adawar cikin gida ta wannan tsarin ne ya janyo arangamar da 'yan ta'addan suka yi a tsakiyar watan Augusta.

HumAngle ta gano cewa, ISWAP ta fara kokarin hadewa tare da karbar mambobin kungiyar ta'addanci Boko Haram bayan wargajewar kungiyar Boko Haram da mutuwar shugabanta, Abubakar Shekau.

Sai dai kash, al'amarin ya gagara sakamakon yawan sojojin da ke garuruwan domin kare shi da kuma juriyar sojojin da ke tafkin Chadi da kusa da tsaunin Mandara.

Kamar yadda rahoton dalla-dalla ya nuna:

"Har yanzu Ba Koura shi ne Sarkin Boko Haram a tafkin Chadi, ya kwace tsibirin Kirta Wulgo tun a ranar 27 ga watan Satumbar shekarar da ta gabata kuma ya kafa rassa a Niger. Aliyu Ngulde na son sake kafa kungiyar a wuraren tsaunikan Mandara."

Rahoton ya bayyana cewa akwai yuwuwar kudin da ISWAP ke samu sun karu bayan karuwar da suke samu a yankin arewa maso gabas.

"Kudaden shigarsu suna zuwa ne daga ragowar yaki, abinda suka tatsa daga jama'a, kamun kifi, noma da kiwo da kuma Zakka."

Rikicin da ke yankin arewa maso gabas ya kai ga rasa rayukan dubban jama'a tare da mayar da sama da mutum miliyan biyu 'yan gudun hijira.

Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya Onyeama Nwachukwu ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis a shafin hukumar na Facebook.

Yace: "Rundunar 25 Birgade karkashin Operation HADIN KAI (OPHK) ta kashe yan ta'addan ISWAP 4 a ranar Laraba, 1 ga Satumba, 2021."

"Yan ta'adan sun yi arangama da Sojoji masu sintiri ne a Kukawa inda akayi musayar wuta har aka kashesu. Sojojin sun kwato bindigogin AK47 guda 4, magazin 4 dauke da albursai kowani guda 30."

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN